Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya ce ba shi da shirin kara farashin man fetur a kasar duk kuwa kara tabarbarewar darajar takardar kudin Naira da ya haddasa tsadar rayuwa.
Karo na biyu kenan da Najeriyar ke karya darajar kudinta cikin kasa da shekara guda, lamarin da ya haddasa hauhawar farashin kayayyaki kari kan matsin rayuwar da jama’a ke fuskanta tun tuni, kuma wannan batu ya sanya fargabar karuwar farashin man na fetur, batun da kamfanin na NNPC ke cewa babu wannan shirin a yanzu.
Read Also:
Sanarwar ta NNPC na zuwa a dai dai lokacin da kiraye-kiraye ke ci gaba da tsananta daga kungiyoyi wajen ganin gwamnatin Najeriyar ta dauki matakan kawo sassauci kan matsin rayuwar da ake ciki, wadannan kungiyoyi kuwa har da na kwadago da suka bayar da wa’adin makwanni biyu ko kuma tsunduma yajin aiki.
A bangare guda kungiyar gwamnonin Najeriyar ta aikewa da gwamnatin tarayya bukatar gaggawa wajen magance matsalar ta tsadar rayuwa baya ga daidaita farashin Naira da kuma uwa uba magance matsalolin tsaron da arewacin kasar ke fama da shi.
A hukumance dai yanzu ana sayar da duk dalar Amurka guda kan Nairar Najeriyar dubu 1 da 531 sabanin 900 da ake sayarwa a makwannin baya, lamarin da ya sake tsawwala tsadar rayuwar da al’umma kef ama da shi.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 39 minutes 18 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 20 minutes 43 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com