Awa 24 bayan shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana hanyoyin dakile matsalar karancin abinci da tsadarsa a kasar, jami’an hukumar da ke kare muradan masu saye ta kasa sun rufe, babban shagon nan na Sahad Stores da ke yankin Area 11 a Abuja.
An dai zargin cewa masu gkatafaren shagon da kara wa abokan huldarsu kudin kaya fiye da farashin da ke makale a jikin kayan.
Read Also:
Da yake yi wa ‘yan jarida bayani, shugaban hukumar mai kare muradan masu saye ta kasa, Adamu Ahmed Abdullahi ya ce wani bincike da hukumar ta gudanar kan katafaren shagon ya nuna musu yadda masu gudanar wa shagon suke “cutar” masu saye.
Ya kara da cewa shagon zai ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa lokacin da za a kammala bincike.
“ Mun fahimci cewa mutanen nan abun da suke yi yaudara ne inda babu gaskiya da yin abu a faifai dangane da farashin kayan da suke da su wanda kuma hakan ya yi karo da sashe na (135) da dokar da ta hana a yaudari abokin hulda ta hanyar cea ka da mai saye ya biya kudin kaya fiye da abin da ke rubuce a kan kayan.” In ji Adamu Ahmed Abdullahi.
PRNijeriya hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 21 minutes 33 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 2 minutes 58 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com