• Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Search
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Sign in
Welcome! Log into your account
Forgot your password? Get help
Password recovery
Recover your password
A password will be e-mailed to you.
PRNIGERIA PRNigeria Hausa
PRNIGERIA PRNIGERIA
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Home Labarai dalilin ECOWAS na Janye takunkumi kan Kasashen Nijar, Mali, Burkina Faso da...
  • Labarai

dalilin ECOWAS na Janye takunkumi kan Kasashen Nijar, Mali, Burkina Faso da Guinea

By
Burkina Faso, Ecowas, Guinea, Mali, Nijar
-
February 24, 2024
Arewa Award

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzkin Ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas ta ɗage tarin takunkuman da ta ƙaƙaba wa ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da kuma Guinea.

Ƙungiyar ta ɗauki matakin ne a wani taron shugabannin ƙasashen ƙungiyar da aka gudanar a Abuja babban birnin Najeriya.

Ƙungiyar ta ce a yanzu za ta iya gayyatar ƙasashen huɗu zuwa tarukanta da suka shafi tsaro da zaman lafiya.

Ecowas ta ce ɗage takunkuman – wanda zai fara aiki nan take – ta yi shi ne bisa dalilai na jin kai.

Huka kuma ƙungiyar ta jaddada kiranta na sakin hamɓararreb shugaban Nijar Mohamed Bazaoum da sojojin ƙasar ke ci gaba da yi wa ɗaurin talala.

Ecowas ta kaƙaba wa ƙasashe takunkuman ne bayan da sojoji suka kifar da gwamnatocin fara hula a ƙasashen.

Daga cikin takunkuman da ƙungiyar ta ƙaƙaba wa ƙasashen sun haɗa da rufe iyakokin ƙasashen da na ƙungiyar da kuma yanke wutar lantarki a Nijar da sauran takunkuman karya tattalin arziki.

Read Also:

  • Bama goyan bayan ayyukan ta’addanci a Najeriya – Miyetti Allah
  • Sojoji sun hallaka ’yan fashi 7 a Katsina
  • Shalkwatar tsaron Nijeriya ta yi karin bayani kan batun kare kai

A makonnin baya-bayan ne ƙasashen Nijar, MAli da Burkina Faso suka ayyana ficewa daga ƙungiyar bayan da suka zargi ƙungiyar Ecowas da ƙaƙaba musu takunkuman karya tattalin arziki.

Ecowas ta riƙa fuskantar matsin lamba daga ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane kan ta ɗage wa ƙasashen takunkuman.

Ko a makon da ya gabata ma tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya Janar Yakubu Gowan wanda shi ne mutum ɗaya tilo da ya rage cikin shugabanin da suka kafa ƙungiyar, ya yi kira ga shugabanninta da su ɗage wa ƙasashen takunkuman.

Nijar ta samu kanta cikin takunkuman Ecowas bayan da sojojin kasar suka kifar da gwamnatin farar hula da Mohamed Bazoum cikin watan Yulin shekarar da ta gabata.

Dama dai masu sharhi sun daɗe suna ta kiraye-kiraye ga shugabannin ƙungiyar su yi kaffa-kaffa, su mai da hankali wajen lalamar ‘ya’yan kungiyar idan ba haka ba garin gyaran gira a rasa ido.

Duk da cewa tun da farko shugabannin kungiyar Ecowas ɗin sun cije a kan matsayinsu na dakatar da kasashen da suka bijire wa demokuradiyyar tare da sanya musu takunkumi,

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Previous articleGwamnatin Nijeriya ta sake bude kantin Sahad na Abuja
Next article‘Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai sama da 100 a jihar Kaduna
Burkina Faso, Ecowas, Guinea, Mali, Nijar

RELATED ARTICLESMORE FROM AUTHOR

Bama goyan bayan ayyukan ta’addanci a Najeriya – Miyetti Allah

Sojoji sun hallaka ’yan fashi 7 a Katsina

Shalkwatar tsaron Nijeriya ta yi karin bayani kan batun kare kai

Gwamnonin PDP na taro a Zamfara

Ya kamata kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarar kare kai – Musa

Hukumar KAROTA ta kaddamar da kotun tafi da gidanka a jihar Kano

kotu ta dakatar da asusun banki huɗu na Mele Kyari

Ana neman mutane 40 a cikin Kogi bayan kifewar kwale-kwale a Sokoto

A biya mu haƙƙoƙinmu, ba mu son bashin gwamnati – ASUU

Amurka za ta sayar wa Nijeriya makamai da kuɗinsu ya kai dala miliyan 346

PDP za ta ƙaddamar da kwamitocin zartaswa na shiyoyi

EFCC ta ba da belin tsohon gwamnan Sokoto Tambuwal da ta tsare

Recent Posts

  • Bama goyan bayan ayyukan ta’addanci a Najeriya – Miyetti Allah
  • Sojoji sun hallaka ’yan fashi 7 a Katsina
  • Shalkwatar tsaron Nijeriya ta yi karin bayani kan batun kare kai
  • Gwamnonin PDP na taro a Zamfara
  • Ya kamata kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarar kare kai – Musa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1529 days 11 hours 40 minutes 24 seconds,



Baptist School Students, Kaduna
1511 days 13 hours 21 minutes 49 seconds

Report By: prnigeria.com/hausa

Book on Sales: Boko Haram Media War: An Encounter with the Spymaster

boko haram

Click Here:To Order Now!

  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
© 2020 PRNigeria. All Rights Reserved.
Latest News
Bama goyan bayan ayyukan ta'addanci a Najeriya - Miyetti AllahSojoji sun hallaka ’yan fashi 7 a KatsinaShalkwatar tsaron Nijeriya ta yi karin bayani kan batun kare kaiGwamnonin PDP na taro a ZamfaraYa kamata kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarar kare kai - MusaHukumar KAROTA ta kaddamar da kotun tafi da gidanka a jihar Kanokotu ta dakatar da asusun banki huɗu na Mele KyariAna neman mutane 40 a cikin Kogi bayan kifewar kwale-kwale a SokotoA biya mu haƙƙoƙinmu, ba mu son bashin gwamnati - ASUUAmurka za ta sayar wa Nijeriya makamai da kuɗinsu ya kai dala miliyan 346PDP za ta ƙaddamar da kwamitocin zartaswa na shiyoyiEFCC ta ba da belin tsohon gwamnan Sokoto Tambuwal da ta tsareMajalisar Dokokin Kano ta Dakatar da Ciyaman din RanoƘananan dillalan mai sun zargi shugabanninsu da yiwa Matatar Dangote zagon ƙasaAtiku Abubakar ya magantu kan tsare Tambuwal da EFCC ta yi
X whatsapp