Home Labarai An yi amfani da sa hannun bogi na Buhari wajen cire sama...

An yi amfani da sa hannun bogi na Buhari wajen cire sama da dala miliyan 6

An tabbatar wa kotu cewa binciken kimiyya ya nuna cewa an yi amfani da sa hannun bogi na tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari wajen cire kuɗi dala miliyan 6.2 don daukar nauyin masu sanya idanu na ƙetare a zaɓukan ƙasar.

Wani shaida da EFCC ta kira, mai suna Bamaiyi Meriga ya tabbatar wa kotu ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Hamza Muazu cewa binciken kimiyya da aka yi wa takardun – da aka sanya hannu a kansu don cire kudin – ya nuna cewa sa hannu da hatimi da aka yi amfani da su wajen cire kudin ba daidai suke da na ainihi ba.

Ya kuma tabbatar da cewa sa hannun ba na tsohon shugaban najeriya Muhammadu Buhari ba ne, kuma ba na tsohon sakataren gamnatin tarayya, Boss Mustapha ba ne.

An gabatar wa alƙalin da ke jagorantar shari’ar takardun biyu, masu ɗauke da umarnin shugaban ƙasa a matsayin shaida, sannan kuma ya amince da su.

Bayan da lauyoyin Emefiele suka nuna ƙorafinsu game da takardun, shaidar ya ce shi ba ma’aikacin EFCC ba ne kuma ba hukumar ce ke biyan sa ba.

Lauyan Emefiele, Matthew Burkaa, ya nuna rashin amincewarsa da shaidar, yana mai cewa shaidar ya yaudari kotun ne don kauce wa tambayoyin da za a yi masa.

To sai dai lauyan masu shigar da ƙara, Rotimi Oyedepo, bai ji dadin kalaman lauyan wanda ake ƙarar ba. An dai ɗage shari’ar zuwa ranar 1 ga watan Maris domin ci gaba da shari’ar.

Emefiele na fuskantar shari’a a kotun kan laifuka 20 da suka ƙunshi zargin cin hanci da haɗin baki da cin amana da amfani da sa hannun bogi wajen cire kudi har dala 6,230,000.

Ana zargin sa da sa hannun bogi na tsohon sakataren gwamnatin ƙasar Boss Mustapha wajen ciye kuɗin ta hanyar da ba ta dace ba.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp