Majalisar Dattijan Najeriya ta dakatar da sanata mai wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya Abdul Ningi daga majalisar na tsawon wata uku bayan zargin shi da furta kalaman da ake ganin sun ‘zubar da ƙimar majalisar.’
A wani zama cike da hatsaniya, majalisar ta bai wa sanatocin damar yin bayani ɗaya bayan ɗaya, inda kusan dukkanin su suka nuna rashin jin daɗi kan kalaman sanata Ningi a wata tattaunawa da kafar BBC.
Tattaunawar da Sanatan yayi da BBC Hausa ta tayar da ƙura a faɗin ƙasar, bayan da ya furta cewa akwai kasafin kuɗin ƙasar kala biyu da ke da su a yanzu.
Ya ce “Bajet (budget) ɗin da aka yi, bayan wanda majalisa ta yi a fili an koma an yi wani bajet a ƙarƙashin ƙasa,”
Ya ƙara da cewa “abubuwan da muka gani sabbi ba mu taɓa jin labarin su, amma har yanzu ƙararru na fannin kuɗi da muka ɗauka suna kawo mana bayanan yadda abubuwan suke faruwa,”
“Misali, an yi bajet na tiriliyan 28 amma mu da muka kididdige sai muka ga bajet ɗinnan kusan tiriliyan 25 ne, ka ga akwai tiriliyan uku, a ina suke?”
Read Also:
Sanata Ningi ya bayyana cewa suna ci gaba da bincike kan lamarin kuma idan suka kamalla za su kai har wurin shugaban ƙasa domin tambayar sa ko yana da masaniya kan abun.
Waɗannan kalamai dai ba su yi wa fadar shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu daɗi ba, inda mai magana da yawunsa ya fitar da sanarwa, inda a ciki ya musanta kalaman sanatan.
Haka nan lamarin ya janyo cece-ku-ce a faɗin ƙasar, saboda ana ganin hakan a matsayin wata fallasa ta badaƙala da ke gudana a ƙarƙashin ƙasa.
A lokacin zaman majalisar na yau Talata an bai wa Sanata Ningi damar yin nasa bayanin, inda ya bayyana cewa bayanin da ake yaɗawa “ya sha bamban da abin da ya faɗa a cikin tattaunawarsa.”
Da farko dai an gabatar da buƙatar dakatar da sanatan na tsawon shekara ɗaya, sai dai daga bisani, sanata Garba Maidoki daga jihar Kebbi ya buƙaci a rage hukuncin zuwa dakatarwa na wata uku, tare da bai wa Ningi damar rubuta takardar neman afuwa.
A ƙarshe majalisar ta cimma matsaya, inda ta yanke wa sanata Ningi dakatarwa ta tsawon wata uku.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 44 minutes 54 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 26 minutes 19 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com