Home Labarai Gwamnatin Kano zata tallafawa maniyatan Jihar da naira dubu dari 5

Gwamnatin Kano zata tallafawa maniyatan Jihar da naira dubu dari 5

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da amincewa da tallafin naira dubu 500 ga maniyyata hajjin bana da suka fito daga jihar, a wani yunƙuri na rage masu raɗaɗin ƙarin kuɗin kujerar hajji da hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya ta yi.

A baya-bayan nan ne hukumar alhazan ta najeriya ta sanar da ƙara kuɗin kujerar hajjin da kusan naira miliyan biyu sai dai ta bayyana cewa ƙarin bai shafi maniyyatan da ke ƙarƙashin tsarin adashin gata ba.

Gwamnan ya bayyana haka ne a shafinsa na X  inda yace  A yanzu duk maniyyaci daga jihar Kano wanda ba ya tsarin adashin gata, zai yi ƙarin naira miliyan ɗaya da dubu ɗari huɗu a maimakon sama da naira miliyan ɗaya da dubu ɗari tara.

Ya ce “duk maniyyacin da ya yi rajista kuma ya biya kafin alƙalamin naira miliyan 4.7 da naira miliyan 4.5 a hukumar alhazai ta jiha a yanzu zai biya naira miliyan 1.4 a maimakon naira miliyan 1.9.”

To sai dai sanarwar gwamnan ba ta fayyace ko tallafin zai kasance ga dukkannin maniyyatan jihar ba ne ko kuma wadanda ba za su iya yin cikon ba.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp