Home Labarai Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da wawashe rumbun ajiyar abinci a jihar

Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da wawashe rumbun ajiyar abinci a jihar

Rahotanni daga jihar kebbi na bayyana yadda wasu mazaunan jihar suka auka cikin wani gidan ajiyar kaya na gwamnati a unguwar Bayan Kara cikin Birnin Kebbi, inda suka wawashe buhunhunan kayan abincin da ke ciki.

Mutanen waɗanda suka bijire wa jami’an tsaron da aka jibge a gidan ajiyar, sun kuma fasa wasu gidajen ajiyar kaya na ‘yan kasuwa da shagunan da ke yankin inda suka saci kayan abinci.

an ruwaito cewa zauna-gari-banzan sun kuma far wa wata babbar mota da aka laftawa kayan abinci dangin hatsi waɗanda aka yi niyyar rabawa a Birnin Kebbi.

Ta ce wawar kayan abinci a gidajen ajiyar kaya irin na Birnin Kebbi, ta faru a Abuja da garin Suleja a cikin jihar Neja.

Hakan na faruwa ne yayin da ake fama da matsalar tsadar rayuwa wanda galibi aka yi imani ya faru ne sanadin cire tallafin man fetur da barin naira ta ƙwaci kanta a kasuwar canji.

jaridar Dailytrust da ake wallafawa a Nijeriya ta ambato Muhammadu Gwadangwaji, shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwar hatsi da ke Bayan Kara a Birnin Kebbi na cewa, “wasu matasa sun ma cinna wuta kan shaguna da gidajen ajiyar kayan ‘yan kasuwa a lokacin wawason.

“(Jami’an tsaro) sun harba harsasai da hayaƙi mai sa hawaye sama, amma su (matasan) ba su razana ba. Sun kutsa kai suka shiga ciki, sannan suka washe gidan ajiyar kayan gwamnati da wasu shagunanmu na ‘yan kasuwa”.

Da yake mayar da martani, Ahmed Idris, wanda shi ne babban sakataren yaɗa labarai ga Gwamna Nasir Idris, cewa ya yi lamarin “abin takaici ne”.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp