Home Labarai Gwamnatin Kano ta kori ma’aikata 3 daga aiki tare da dakatar da...

Gwamnatin Kano ta kori ma’aikata 3 daga aiki tare da dakatar da wasu

Hukumar kula da asibitocin jihar Kano ta amince da korar wasu ma’aikata tare da dakatar da wasu ma’aikatan na babban asibitin Karamar Hukumar Kabo nan take, bayan samunsu da lefin Cazar kudade daga marassa lafiya da suka wuce Kima da sauran lefuka.

Asibitin wanda babban sakataren hukumar da babban darakta na cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta jihar Kano (KNCDC) Dr. Muhammad Abbas, da darakta janar na CSACA Dr. Usman Bashir suka ziyarce su gaba daya sun nuna bacin ransu ga abinda ya faru tare da amincewar daukar matakin.

Shugaban hukumar Dakta Mansur Mudi Nagoda ya bayyana hakan jim kadan bayan sanya hannu kan amincewar da hukumar ta gabatar bayan kammala ziyarar da suka yi a asibitin.

Dakta Nagoda ya yi bayanin cewa an kama jami’ai 3 na sashen X-ray suna cajin marasa lafiya 12,000 na gwajin X-ray maimakon farashin asibiti da aka amince da shi na 2,000 kuma babu wata takarda da za ta nuna a matsayin shaidar biyan kuɗin da ke barin wurin don aiwatar da gwajin, lamarin da yasa ake X-ray 10 kacal a kowanne mako duk da cewa Injinan Asibitin na X-ray 2 suna aiki. Daga nan sai ya amince da korar jami’an 3 nan take.

Haka kuma, shugaban Hukumar ya amince da dakatar da akawun Asibitin da mai binciken kudi da shugaban dakin gwaje-gwaje saboda sayar da kayan gwajin cuta mai karya Garkuwar jikin Dan Adam wanda kyauta gwamnatin jihar ta ba wa cibiyoyi kuma an umarce su da su kai kansu ga hedikwatar hukumar don ci gaba da ladabtar da su.

Bugu da kari, Dakta Nagoda ya bayyana cewa dakin karbar Haihuwa na Asibitin ba shi da tsari domin ba shimfidar gado a kan gadaje, babu wani jami’in kula da gurin, haka kuma an wulakantar da wasu kayayyakin kula da lafiyar Alumma wanda wani majalisa ya bayar da gudummawar shekaru 4 da suka gabata, tare da nuna halin ko in kula da kayayyakin yaki da cutar COVID-19.

Shugaban ya kuma ce abin bakin ciki ne bayan mai girma gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa ya dawo da kowane ma’aikacin lafiya a kan ma’aunin albashin CONHESS, amma duk da haka suna cin zalin Marassa Lafiya tare.

Jami’ar hulda da jama’a ta hukumar Samira Suleiman ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Kano ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce shugaban ya yi kira ga maaikatan hukumar da su rika gudanar da ayyukansu don cigaba da kula da lafiyar Alummar Kano.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp