Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa ba ta ciyo rancen kuɗi naira biliyan 14.26 ba, sai dai kuɗin wani ɓangare ne na kuɗaɗen da gwamnatin da ta shuɗe ta ciyo na naira biliyan 20.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin jihar ta Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, inda ya ce gwamnati ba ta ci wani bashi a gida ko waje ba tun bayan hawan Gwamna Dauda Lawal.
A makon jiya ne hukumar kula da basuka ta Najeriya ta fitar da rahoto game da gwamnonin da suka ci bashi a cikin wata shida.
Rahoton ya ce sababbin gwamnonin jihohi 13 na ƙasar ciki har da Kano, da Zamfara, da Katsina da Sokoto da Kaduna sun ci bashin naira biliyan 226 daga masu bayar da bashi a ciki da wajen ƙasar, bayan rantsar da su a watan Mayun 2023.
Hukumar ta kuma ce ta haɗa alƙaluman ne bayan jimillar lissafin da suka yi kan farashin dala a kan naira 889.
Amma gwamnatin jihar Zamfara ta musanta hakan inda ta ce, “Muna so mu fayyace rahoton ofishin kula da basuka (DMO) cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ciyo bashin Naira biliyan 14.26.
“Gwamnatin jihar Zamfara ba ta taɓa neman buƙatar karɓar rance ba ko tuntuɓar majalisar jiha ko ta ƙasa domin neman wannan buƙata,” in ji sanarwar.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 10 minutes 54 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 52 minutes 19 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com