Home Labarai Gwamnan Kano ya sake nada Oga Boye a mukami

Gwamnan Kano ya sake nada Oga Boye a mukami

Gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sake yin sabbin nade-nade a cikin kunshin gwamnatin jihar.

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa.

Sanarwar ta ayyana Farfesa Ibrahim Magaji barde matsayin mai bada shawara na musamman ga mai girma gwamna fannin harajin cikin gida.

  1. Dr. Abdulhamid Danladi, mai bawa Gwamnan shawara kan ‘yan kano mazauna ketare na II
  2. Engr. Bello Muhammad Kiru, Mai bada shawara na musamman fannin Albarkatun ruwa.
  3. Yusuf Shuaibu Imam (Ogan Boye) da aka sake nadawa matsayin Mai bada shawara na Musamman kan matasa da wasannan.
  4. Sai kuma Dr. Nura Jafar Shanono da aka matsar daga matsayin Mai bada shawara na musamman a fannin Albarkatun ruwan, zuwa babban managan hukumar (WRECA).
  5. haka kuma sanarwa ta bayyana daga likkafar Hon. Baba Abubakar Umar daga mai bada shawara na musamman zuwa babban sakataren hukumar dake lura da makarantu masu zaman kansu na jihar kano.
  6. An kuma nada Hon. Nasir Mansur Muhammad a matsayin babban daraktan dake lura da kanana da matsakaitan sana’oi (SMEs)
  7. Aminu Hamidu Bako Kofar Na’isa zai zama mataimakin babbana daraktan (DMD), a ma’aikatar aikin gona da cigaban karkara ta (KNARDA).

haka kuma an nada Engr. Mukhtar Yusuf, matsayin mataimakin babban daraktan (DMD) a hukumar (WRECA).

Daga bisani sanarwar ta tabbatar da cewa nadin ya fara aiki nan take, tare da fatan kammalawa lafiya da nasara.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp