Home Labarai Sojojin Saman Nijeriya sun sake hallaka Kwamandan ISWAP a Jihar Borno

Sojojin Saman Nijeriya sun sake hallaka Kwamandan ISWAP a Jihar Borno

Nigeria Airforce

Wani harin dakarun sojin saman Nijeriya karkashin Operation Hadin kai (OPHK) yayi sanadiyyar tarwatsa maboyar mayakan kungiyar ISWAP a kauyen Kulleram dake yankin tafkin Chadi.

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai da bayanai na rundunar sojin saman Nijeriya Air Vice Marshal Edward Gabkwet ya fitar mai dauke da kwanan wata 16 ga watan Afrilun 2024.

Sanarwar ta ce dakarun sun gudanar da harin ne a ranar 13 ga watan Afrilun 2024, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mayakan masu tada kayar baya kimanin 30, wanda cikin su harda manyan kwamandoji da suka hadar da Ali Dawud, Bakura Fallujah, da Malla Ari.

Haka kuma yayin harin dakarun sun sami nasarar tarwatsa maboyar ‘yan ta’addan, baburan hawa da wasu kayan aikin ‘yan ta’addan masu tarin yawa.

Rahotannin sirri dake fitowa daga yankin na kulleram wanda ke matsayin  wata cibiyar hada-hada wanda ciki har da sarrafa kayan masarufi.

Sanarwar tace atisayen rundunar sojin saman ya nuna yadda runudnar sojin ta mayar da hankali wajen ganin ta kawar da  matsalolin rashin tsaro dake addabar Al’ummar Nijeriya.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp