Home Labarai Sojojin Nijeriya Sun tarwatsa maboyar ‘yan ta’adda a jihar Zamfara

Sojojin Nijeriya Sun tarwatsa maboyar ‘yan ta’adda a jihar Zamfara

Sojojin Nijeriya sun sami nasarar tarwatsa maboyar ‘yan bindiga a karamar hukumar Maru dake jihar Zamfara.

Wannan na kushe ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar sojojin Nijeriya Manjo Janar Onyema Nwachukwu, wadda ya fitar ranar talaka aka raba ga manema labarai.

Sanarwar tace dakarun sojin sun yi nasara hallaka ‘yan ta’adda 12 a karamar hukumar ta Maru, tare da tarwatsa maboyar su, bayan samun wasu bayanan sirri da suka kan ‘yan bindigar.

Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun hallaka mayakan 12 bayan musayar wuta da su yi, in da wasu kuma suka tsere cikin daji da raunin  harbi a jukkunan su.

Haka kuma dakarun sojin sun sami nasarar kwato bindiga kirar AK 47, baburan hawa, bindiga kirar gida da sauran muggan makamai.

Jihar Zamfara na guda cikin jihohin arewacin Nijeriya dake fama da matsalar rashin tsaro, sakamakon ‘yan bindiga masu satar mutane domin karbar kudin fansa, wadanda ke aukawa garuruwan jihar.

PRNigeria Hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp