Home Labarai Sojojin Nijeriya sun bankado maboyar mayakan ISWAP a jihar Borno

Sojojin Nijeriya sun bankado maboyar mayakan ISWAP a jihar Borno

Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun sami nasarar bankado maboyar mayakan boko haram tsagin ISWAP a jihar Borno dake Arewa maso gabashin kasar.

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran rundunar sojin Nijeriya Manjo Janar Onyema Nwachukwa ya fitar aka raba manema labarai.

Sanarwar ta ce dakarun rundunar karkashin “operation Desert Sanity III” sun kai wani harin ta sama da kuma makaman atilare a hannu guda da wasu dakru na musamman a kauyukan Ngumne, kawaran da Mangu dake dajin sambisa da yankin Timbuktu.

Yace dakarun sojin sun yi bata-kashi da mayakan boko haram inda suka yi amfani da wasu makamai masu fashewa kan mayakan na ISWAP, wannan ta sanya suka ci karfin mayakan inda suka ranta a na kare.

Nwachukwa ya kara da cewa dakarun sojin sun sami nasarar kwato manyan makamai, da suka hadar da motar dake daukan bindigu, bindigar kirar 105mm howitzer, haka kuma sun tarwatsa maboyar mayakan na ISWAP.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp