Ƴan sanda tare da haɗin gwiwar ƙungiyar mahauta a Bauchi sun kashe mutum takwas da ake zargin masu garkuwa da mutane ne yayin musayar wuta a kusa da iyakar jihar da Filato.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda ta jihar Bauchi SP Ahmed Wakil ya bayyana wa ƴan jarida a jihar a ranar Alhamis cewa ƴan sanda sun samu nasarar ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su don karɓar kuɗin fansa.
Read Also:
Sanarwa da mai magana da yawun hukumar ya fitar ta bayyana cewa “Jami’an na ƴan sanda da aka kawo daga offisoshin ƴan sanda na Gumau da Tilde da Tulu sun haɗu da masu garkuwa da mutane tare da makamansu yayin da suke bakin aikinsu na tabbatar da tsaro inda suka yi musayar wuta da ya yi sanadiyyar kashe masu garkuwar huɗu.
“Biyu daga cikin waɗanda ake zargin da suka mutu daga bisani sun amsa laifin garkuwa da mutane da dama a Bauchi da Filato da ya haɗa da mummunan kisan gillar da aka yi wa maigarin Ruruwai a garin Lame dake ƙaramar hukumar Toro.
“Yayin musayar bindiga tsakanin jami’an da sauran masu garkuwar da ke gadin mutanen da aka yi garkuwa da su aka sake kashe mutum huɗu cikinsu sannan aka samu ƙwato mutum ukun da ke hannunsu ba tare da biyan kuɗin fansa ba”.
SP Wakil ya yi kira ga al’umomin garuruwan Bauchi da su ba da haɗin kai da jami’an tsaron ta hanyar samar musu da bayanan sirri da za su taimaka wajen shawo kan matsalolin tsaro kafin ma su faru wanda faruwar tasu kan iya samar da mummunan lahani a kan rayuka da kuma dukiyoyi.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 32 minutes 29 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 13 minutes 54 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com