Home Labarai ‘Yan sandan a Kano sun kama masu kwacen waya

‘Yan sandan a Kano sun kama masu kwacen waya

Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta tabbatar da kama matasa hudu da take zargi da yiwa mutane kwacen waya a jihar.

wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wadda ta ce an kama mutanen kan titin Airport Road inda kuma aka same su da wayoyin hannu guda bakwai da ankwa.

Mutanen da ake zargi sun bayyana cewa suna amfani da babur mai ƙafa uku wajen yi wa jama’a ƙwacen waya.

Rundunar ta ce wani Aminu Sulaiman ya shigar da ƙorafi cewa an sace wayarsa cikin motarsa a wani gidan mai da ke jihar inda bayan samun rahoton, wata tawagar ƴan sanda ta kama mutane uku da ake zargi. An gano wayar da aka sace da kuma babur mai ƙafa uku da suke amfani da shi wajen aikata ta’asar.

A cewar rundunar a ranar 23 ga watan Afrilu, sun samu kiran waya inda aka sanar da su wasu ɓatagari a kan babur mai ƙafa uku suna far wa fasinja tare da sace wayarsa. An kuma aika tawagar ƴan sanda inda suka fara bincike sannan suka kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi tare da gano wayar da wuƙa mai kaifi daga wajensa.

Rundunar ta ce ana gudanar da bincike kan mutanen da ake zargi a sashen binciken manyan laifuka sannan daga bisani za a gabatar da su gaban kotu.

Abdullahi kiyawa facebook Page
Abdullahi kiyawa facebook Page

Abdullahi kiyawa facebook Page

Ko dai a ranar bikin hawan Nasarawa da aka gudanar cikin bukukuwan karamar sallah a jihar, Gwamna Abba kabir Yusuf ta cikin jawabinsa ya zargi wasu cikin ‘yan siyasa da bayar da gudunmawa wajen haifar da fadan daba da rikicin siyasa a jihar.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp