Home Labarai An samar da ‘yan sanda da za suyi gadin makarantu a jihar...

An samar da ‘yan sanda da za suyi gadin makarantu a jihar Kano

Rundunar Yan Sandan Jihar Kano ta Samar da wata runduna ta musamman da zata Sanya Idanu akan Makarantun Dake Jihar Kano

Kwamishinan Yan Sandan Jihar Kano CP. Muhammad Ussaini Gumel shine ya Kaddamar da Rundunar a shelkwatar Yan Sandan Dake unguwar bompai a jihar

Aikin Rundunar shine Tabbatar da Tsaro a Makarantun da ake dasu a Kano, da Kuma Kai Dauki a duk Lokacin da aka Bukaci Hakan.

A cewar kwamishinan Yan Sandan Matakin Samar da Wannan rundunar, ya biyo bayan Umarnin Babban Sifetan Yan Sandan Nigeria Kayode Egbetokun, da ya Bukaci kowane kwamishinan Yan sanda ya Samar da irin Wannan runduna Domin baiwa Makarantun kariya

Haka kuma ya Bukaci Jami’an da aka zabo, suka Kuma samu horo da Suyi Aiki Tukuru Wajen Sauke Nauyin da aka Dora Musu, na kare lafiya da dukiyoyin al’umma

Jami’an zasuyi aiki kafada da kafada da Sauran Baturen Yan Sandan Dake Shiyyar da aka Tura su Domin aiki tare.

Haka Kuma an Samar da Motoci da Babura ga Jami’an Yan Sandan da zasuyi Wannan aiki na Tabbatar da Tsaro a Makarantun Dake Jihar Kano.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp