Home DUNIYA Ƴan sanda sun cafke matashin da ake zargi da cinna wa masallaci...

Ƴan sanda sun cafke matashin da ake zargi da cinna wa masallaci wuta a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta cafke wani matashi da ake zargi da cinna wa wani masallaci wuta a lokacin da mutane fiye da 30 ke sallar Asuba a ciki. lamarin dai ya faru ne a a ƙauyen Larabar Abasawa a ƙaramar hukumar Gezawa.

wannan na kunshe ta cikin wata sanarwar da rundunar ta fitar, mai dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce matashin mai suna Shafi’u Abubakar mai shekara 38 ya yi sanadiyyar ƙonewar mutane.

Tuni dai aka kwashe mutum 24 waɗanda suka ƙone zuwa asibiti domin a duba lafiyarsu.

SP Kiyawa ya ƙara da cewa binciken da aka gudanar dai ya nuna cewa an yi amfani da man fetir ne wajen cinna wutar.

Dangane kuma da dalilin faruwar al’amarin, SP Kiyawa ya ce “matashin ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon ƙin raba gado a tsakanin danganinsa, inda ya ce waɗanda suka zalunce shi ɗin suna cikin masallacin a lokacin da suke sallah. Kuma ya yi hakan ne domin ya aike da saƙo.” In ji matashin.

PRNigeria Hausa
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp