Home General Mayakan ISWAP sun Hallaka DPO a Jihar Borno

Mayakan ISWAP sun Hallaka DPO a Jihar Borno

Rahotannin daga jihar Borno dake Arewa maso gabashin Nijeriya na bayyana cewa wasu da ake zargin mayakan kungiyar boko haram tsagin ISWAP sun hallaka baturen dan sanda Sunday Pius a karamar hukumar Marte dake jihar.

Haka kuma harin ‘yan ta’addan yayi sanadiyyar raunata wasu jami’an ‘yan sanda guda biyu.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwa lamarin ta bakin Kakakin ta ASP Kenneth Daso ya a birnin Maiduguri a yammacin ranar talata.

ASP Kenneth yace sun sami kiran gaggawa cewa ‘yan ta’addan sun hallaka baturen ‘yan sanda dake lura da yankin New Marte a ranar Litinin wannan ne ya sanya kwamishinan ‘yan sandna jihar ya bada umarni yin bincike.

An ruwaito cewa mayakan sun shiga cikin garin ne da misalign karfe 7 da mintuna 30 na daren ranar litinin, in da suka kai hari kan jami’an lafiya, sai dai an ruwaito jami’an lafiyar sun tsallake rijiya da baya.

Bayan da jami’an lafayar sukayi gudun tsira zuwa ofishin ‘yan sandan ne ‘yan ta’addan suka afkawa ofishin nan suka hallaka baturen ‘yan sandan tare da raunata jami’an ‘yan sanda guda biyu.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp