Ƙungiyoyin ƴan ƙwadago na NLC da TUC sun sassauta abin da suke buƙata gwamnati ta biya a matsayin mafi ƙarancin albashi a ƙasar zuwa naira 497,000.
A baya dai ƙungiyoyin ƙwadagon sun ce amince da naira 615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi da suke son gwamnatin ƙasar ta amiince da shi.
Read Also:
Yayin cigaba da tattaunawar a ranar Talata, ƙungiyoyin sun kuma yi watsi da sabon ƙudirin da gwamnati ta gabatar na naira 54,000 a matsayin albashi mafi ƙaranci.
Haka kuma a ranar Laraba kwamitin ƙarin albashin ya bai wa NLC tayin naira 57,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin, inda nan take ƙungiyar ƙwadagon ta yi fatali da tayin.
PRNigeria Hausa