Za’a sake zaben sarki a Kano

Majalisar dokoki ta jihar Kano ta amince da rushe duka masarautun jihar bayan soke sabuwar dokar da ta ƙirƙiri sababbin masarautu a 2019.

Hakan na nufin cewa an koma amfani da tsohuwar dokar da ta kafa masarautar Kano.

Majalisar ta ɗauki matakin ne a zaman da ta yi ranar Alhamis.

Sabon matakin da majalisar ta ɗauka ya nuna cewar sarakunan jihar biyar na Kano, da Bichi, da Ƙaraye, da Gaya, da Rano duk sun rasa kujerunsu.

Idan har Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu a kan sabuwar dokar hakan zai ba shi damar naɗa sabon sarki a masarautar Kano.

PRNIgeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1485 days 23 hours 2 minutes 34 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1468 days 43 minutes 59 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com