Kwankwaso – bani da Hannu a rushe masarautun Kano

Jagoran jam’iyyar NNPP a Najeriya kuma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ba shi da hannu a rushe masarautun jihar da gwamnatinsu ta yi ranar Alhamis.

Ana yi wa Kwankwaso kallon babban jagora kuma mafi ƙarfin faɗa-a-ji a ɓangaren siyasar Kwankwasiyya na jam’iyyar NNPP, wadda ke mulkin Kanon a yanzu.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya rushe masarautun biyar ne bayan ‘yan majalisar dokokin jihar sun rushe dokar da magabatansu suka ƙirƙira a 2019 ƙarƙashin gwamnatin Abdullahi Ganduje ta jam’iyyar APC.

Soke dokar ta sa aka tuɓe duka sarakunan jihar biyar kuma nan take gwamnan ya bayyana sunan Muhammadu Sanusi II (ko kuma Sanusi Lamido Sanusi) a matsayin sabon sarki bayan masu naɗin sarki sun zaɓe shi.

ta cikin tattaunawa da yayi da manema labarai kwankwaso ya bayyana cewa yanzu haka yana Abuja kawai labarin ya samu kamar yadda kowa ya gani a kafafen yada labarai

“Ni dai ga ni a Abuja, abin da ka gani ni ma shi na gani,”

Ya ƙara da cewa sai a ranar Juma’a ne yake sa ran zuwa birnin na Kano, wadda za ta iya yin daidai da ranar da Sarki Muhammadu Sanusi II zai koma kan karagar mulkin Kano.

“Zan yi magana da ‘yan majalisar da shi gwamnan don mu ji yadda abubuwan suke,” in ji shi.

Sai dai tun a watan Janairun da ya gabata Kwankwaso ya tabbatar da cewa babu shakka za a sake nazari kan dokar da ta kafa sabbin masarautun huɗu a Kano.

“Gaskiya yana ɗaya daga cikin abubuwan da ba a taɓa zama da ni a kai ba, amma kuma nasan dole za a zo a yi magana,” kamar yadda ya bayyana a lokacin.

“Da ma ba cewa na yi a yi dama ko a yi hagu ba, cewa na yi za a duba kuma ga shi sun duba.”

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1189 days 15 hours 17 minutes 2 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1171 days 16 hours 58 minutes 27 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com