Kungiyoyin NLC da TUC zasu tsunduma yajin aiki

Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na TUC da NLC a Najeriya sun yanke shawarar tsunduma yajin aikin sai baba ta gani sakamakon rashin cimma yarjejeniya tsakaninsu da gwamnatin tarayya.

Gamayyar ƙungiyoyin sun sanar da hakan ne da yammacin ranar Juma’a bayan wani taro da suka yi inda suka tattaunawa yiwuwar tsunduma yajin aikin.

A farkon makon nan ne dai manyan ƙungiyoyin ƙwadago guda biyu suka yi watsi da tayin naira 60 da gwamnatin tarayya ta yi masu a matsayin albashi mafi ƙanƙanta, biyo bayan zaman da suka yi da gwamnatin tarayya, inda a nan ne gwamnatin ta yi tayin.

Da farko dai sai da gwamnatin Najeriyar ta fara kara naira dubu uku a kan tayin naira dubu 47 da ta yi a baya.

Su ma ƙungiyoyin ƙwadagon sun rage dubu uku daga naira 497 da suke nema a matsayin albashi mafi ƙanƙanta.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 12 hours 32 minutes 20 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 13 minutes 45 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com