Rahotannin na bayyana cewa kotu ta bayar da belin dakataccen mataimakain kwamishinan ‘yan sanda shugaban rundunar kai daukin gaggawa Abba Kyari, bayan zaman gidan gyaran hali na watanni 27.
Wannan na zuwa ne bayan hukuncin babbar kotun tarayya dake zamanta a birnin tarayya Abuja na bashi belin makwanni biyu.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Kotun ta ce an bayar da belin Abba kyari ne domin ya je gida ya kammala jana’idar Mahaifiyar.
Kotun data zauna ranar juma’a 31 ga watan mayun daya gabata, domin duba bukatar bayar da belin Kyari dake fuskantar tuhume-tuhume na ta’ammali da miyagun kwayoyi, biyo bayan kama shi da akayi a watan fabrerun shekarar 2022.
Kakakin hukumar kula da gidan gyaran hali da tarbiyya na birnin tarayya Abuja Admu Duza yace an bayar da belin kyari ne bayan ya cika wasu sharudda.
PRNigeria Hausa











