Home General Sojojin Nijeriya sun hallaka Dan Ta’adda Buharin Yadi

Sojojin Nijeriya sun hallaka Dan Ta’adda Buharin Yadi

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar shahararren dan ta’addan nan wanda ya addabi arewacin Nijeriya Buharin Yadi.

Wannan dai na kunshe ta cikin wata mai dauke da sa hannun kwamishinan tsaro da Al’amuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan.

Wani barin wuta da dakarun sojojin Nijeriya na rundunar Operation Whirl Punch sukayi kan  maboyar dan ta’addan Buhari Alhaji Halidu wanda aka fi sani da (Alias Buharin Yadi) ta yi sanadiyyar mutuwar sa da wasu cikin mayakan sa a maboyar su.

Dakarun sojojin dake karkashin kwamandan sojoji dake lura da iyakar kananan hukumomin Giwa da Sabuwa dake Jihohin kaduna da Katsina Manjo Janar MLD Saraso, sun sami nasarar ne a daidai Idasu bisa wasu bayanan sirri da suka samu kan mayakan dake sintiri a yankunan Samunaka, saulawa dake jihar Katsina.

Bawan wani batakashi daya gudana tsakanin dakarun da mayakan bayan bankado maboyar su da dakarun sukayi abinda ya haddasa mutuwar shanu masu tarin yawa.

Kachalla buhari Alhaji Haladu wanda aka fi sani da Buharin Yadi ko kuma Buhari Janar da saran tawagar sun uzzirawa yankunan Kidandan/Galadimawa dake karamar hukumar, Sabon Birni/Kerawa dake karamar hukumar Igabi, Sabuwa dake jihohin Katsina Niger da Zamfara.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp