Home General Ma’aikatan PSC sun bukaci Tinubu ya Cire IG Egbetokun

Ma’aikatan PSC sun bukaci Tinubu ya Cire IG Egbetokun

Gamayyar kungiyoyin Ma’aikatan hukumar dake lura da ayyukan ‘yan sanda ta Nijeriya PSC ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu daya sauke shugaban rundunar ‘yan sandan kasar Kayode Egbetokun bisa yunkurin yin kafar ungulu a shirin daukar jami’an hukumar.

Yayin da take ganawa da manema labarai a birnin Abuja ranar laraba kungiyar ta zargi wasu cikin manyan jami’an hukumar da yunkurin cusa sunayen wadanda basu cancanta ba a lokacin jarabawar daukar aikin.

Mambobin kungiyar dake rera wakokin zanga – zanga, sun bayyana yunkurin rundunar ‘yan sandan na  na dauke hankula.

Kungiyar tace  NPF na kokarin kare shugaban kasa kada ya fahimci rashin shirin makarantun horar da ‘yan sanda da yadda suke a mawuyacin hali.

Wannan dai na zuwa ne bayan da hukumar dake lura da ayyukan ‘yan sanda ta saki sunayen mutum dubu 10 wadanda suka sami nasarar haye jarabawar daukar aikin dan sanda a Nijeriya.

Sai dai daga bisani hukumar ‘yan sandan ta yi fatali da jerin sunayen wanda tace akwai ayyukan damfara a cikin sa.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp