Home DUNIYA NCDC ta ce bata da wadatacciyar Allurar Rigakafin Kwalara

NCDC ta ce bata da wadatacciyar Allurar Rigakafin Kwalara

Hukumar dake dakile yaduwar cuttukka ta Nijeriya NCDC tace bata da wadatacciyar Allurar ragakafin cutar kwalara.

Daraktan hukumar Dr. Jide Idris ne ya bayyana hakan, inda yace kasar ta bayar da sallahun allurar ga hukumomin dake da alhakin sayar da ita a duniya da masu bayar da tallafinta, duk da cewa bai bayyana ranar da allurar zata iso ba.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rahotannin ke bayyana yadda mutane 40 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar ta kwalara a kasar nan.

Dr. Jide ya bukaci al’ummar kasar nan da su yi amfani da allurer rigakafin da wasu matakan kariya daga kamuwa da cutar ta kwalara.

Cutar kwalara dai na guda cikin cututtukan da ake daukar su ta hanyar shan ruwa ko abinci maras tsafta, wanda takan kai ga hallaka mutun bayan kamuwa da ita.

Bincike dai ya nuna cewa a cikin shekaru hudu da suka gabata cutar ta hallaka mutane 4,364 yayin da aka zargi mutane 139,730 da suka kamu da cutar a kasar nan.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp