Shugaban sojojin Nijeriya Laftanal Janar Taoreed Lagbaja yace dakarun dake yaki da ayyukan ta’addanci da sauran lamaurran da suka shafi tsaro a yankin Arewa maso gabashin kasar na samun gagarumar nasara.
Lagbaja ya bayyana hakan ne a ranar alhamis a garin Jos, yayin da yake ganawa da manema labarai, a wani bangare na bikin cikar shekara da rundunar ta shirya.
ya dora alhakin harin kunar baki wake a Gwozo bisa hare haren da dakarun sojoji suka din gi kaiwa kan mabambanta gungun ‘yan ta’addan a yakin na arewa maso gaba.
Read Also:
yace: “Ana sake samun nasarori bisa yadda dakarun ke cigaba da matsa kaimi da kuma wasu hare hare kan ‘yan ta’addan dake yankin.
Ya kara da cewa sun sami bayanan sirri dake nuna yadda ‘yan Ta’addan suka shirya kai hare-hare kunar bakin wake har guda 15 amma 3 ne kawai suka sami nasara.
“Dakrun mu sun yi dukkanin mai yiwuwa don gani sun kawar da makiya.
“Don haka, ina kira ga Al’ummar Nijeriya da su zama masu taimakawa harkokin tsaro, zamu tabbatar da bincikar dukkanin wani taron al’umma,” a cewar sa.
ya bayyana yaki da rashin tsaro matsayin abinda ke bukatar hada karfi da karfe, “don haka ya kamata mu dauke shi da matukar muhimmanci”.
(NAN)
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 42 minutes 46 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 24 minutes 11 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com