Duk da cewa Messi baya cikin kasashen Nahiyar Turai da ke fafatawa a gasar Euro 2024 amma hakan bai hana kara sabunta kansa da daukakar da yake da ita a idon duniya ba.
Ɗan wasan gaban Inter Miami Lionel Messi ya jagoranci tawagar Argentina zuwa wasan ƙarshe na gasar Copa America bayan ta doke Canada da ci 2-0.
Ɗan wasan mai shekaru 37 da haihuwa ya zura ƙwallo a minti na shida bayan an dawo daga hutun rabin lokaci bayan ɗan wasan gaba na Manchester City Julian Alvarez, ya fara ci wa Argentina a minti na 22 da fara wasa.
Wannan shi ne karo na shida cikin gasa takwas na baya bayan nan da Argentina ta kai matakin wasan ƙarshe a gasar, kuma Messi ya bayyana cewa burinsa a yanzu shi ne ya ga cewa Argentina ta lashe gasar.
Read Also:
Ya ce: ‘Ba abu ne mai sauƙi ba ne sake samun damar buga wasan ƙarshe ba, don sake fafatawa don zama zakara’.
Wasan ƙarshen da za su fafata da Uruguay ko Colombia, zai kasance wasan ƙarshe da Angel di Maria zai buga wa Argentina kafin ya yi ritaya daga buga wasa sannan kuma har yanzu akwai shakku kan makomar Messi.
Amma kocin tawagar Argentina Lionel Scaloni ya ce zai yi ƙoƙarin shawo kan Di Maria da Messi su ci gaba da bugawa Argentina wasanni.
‘Batun Leo kusan iri ɗaya ne da na Angel,’ in ji Scaloni.
“Dole ne mu bar shi ya yanke ta shi shawarar kuma ba za mu taba zama wadanda za su rufe kofa ba, zai iya kasancewa tare da tawagarmu har tsawon lokacin da yake so. Kuma idan yana so ya yi ritaya amma duk da haka ya zo ya ci gaba da tallafa mana a wani mataki, abu ne da za mu yi maraba da shi’.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 11 hours 53 minutes 45 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 35 minutes 10 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com