Home DUNIYA Kotun Koli ta haramtawa Gwamnatocin jihohi rike kudaden kananan hukumomi

Kotun Koli ta haramtawa Gwamnatocin jihohi rike kudaden kananan hukumomi

Kotun Ƙolin Najeriya ta ce riƙe kuɗin ƙananan hukumomi da gwamnaonin jihohin ƙasar ke yi ya saɓa wa kundin tsarin mulki.

Cikin hukuncin da ta yanke kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Emmanuel Agim, ya ce kotun ta fahimci cewa gwamnatocin jihohin ƙasar sun shafe fiye da shekara 20 ba tare da sakar wa ƙananan hukumomin mara ta fuskar kuɗaɗensu ba.

Alƙalin kotun ya ci gaba da cewa tun tsawon wannan lokaci, ƙananan hukumomin ba sa samun kuɗaɗen da ya kamata su samu daga gwamnonin jihohin ba, waɗanda ke kashe kuɗin ta hanyar yin ayyuka a madadin ƙananan hukukomin.

Mai shari’a Agim ya ce dole ne ƙananan hukumomin ƙasar 774 su riƙa amfani da kuɗaɗensu da kansu ba tare da sa katsalandan daga gwamnonin jihohi ba.

Haka kuma alƙalin ya yi watsin da ƙorafin da gwamnonin suka yi ta bakin lauyoyinsu.

Gwamnatin tarayyar ta kuma buƙaci kotun ta dakatar da gwamnonin jihohin ƙasar, daga rushe zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp