Home DUNIYA Tinubu ya nada sabon shugaban Hukumar NPA

Tinubu ya nada sabon shugaban Hukumar NPA

Shugaban kasa Bola Tinubu ya naɗa Abubakar Ɗantsoho matsayin sabon Shugaban Hukumar Tashoshin Ruwa ta NPA.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Ajuri Ngelale ya fitar a Yammacin Juma’ar.

Naɗin Ɗantsoho na zuwa ne bayan sallamar Mohammed Bello-Koko daga shugabancin hukumar tashoshin ruwa kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Kazalika, sanarwar ta ce Tinubu ya kuma naɗa tsohon Sanatan Ekiti ta Kudu kuma tsohon Ƙaramin Ministan Ayyuka, Dayo Adeyeye a matsayin sabon Shugaban Majalisar Gudanarwar hukumar ta NPA.

Kafin naɗinsa, Ɗantsoho ya riƙe muƙamai daban-daban a hukumar ciki har da muƙamin babban manaja ne hukumar ta NPA.

Dukkan su za su fara aiki ne nan take, kamar yadda sanarwar Fadar Shugaban Kasar ta bayyana.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp