Home DUNIYA Rundunar Sojojin Saman Nijeriya ta tarwatsa maboyar ‘yan ta’adda a jihar Kaduna

Rundunar Sojojin Saman Nijeriya ta tarwatsa maboyar ‘yan ta’adda a jihar Kaduna

Rundunar Sojojin saman Nijeriya tace ta sami nasarar tarwatsa maboya ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, a garin kufam shantu dake karamar hukumar giwa dake jihar kaduna a arewa maso yammacin kasar Nijeriya.

Wannan na cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na rundunar Air vice Marshal Edward Gabkwet ya fitar a ranar lahadi.

Sanarwar ta ce daya daga cikin atisayen da rundunar sojin ta kai a ranar 12 ga watan Yuni a maboyar ‘yan ta’adda ta Alhaji layi, wadda suka sami nasarar tarwatsa ta da kuma kometa.

Haka kuma a wani harin makamancin wannan da rundunar ta gudanar ranar 13 ga watan na Yuni kan ‘yan bindigar a cikin dajin malum dake karamar hukumar Igabi, wadda rundunar ta ce ta sami gagarumar nasara.

Jihar kaduna dai na guda cikin jihohin dake arewacin Nijeriya dake fama da matsalolin rashin tsaro da suka addabi al’ummar ta musamman masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.

PRNigeria hausa

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp