Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta dage haramcin shiga ƙasarta da ta yi wa ‘yan Nijeriya.
Wannan na cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar wacce PRNigeria Hausa ta samu mai dauke da sa hannun Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai na Kasa, Mohammed Idris, a ranar Litinin.
Read Also:
Sanarwar ta ce bayan wata tattaunawa da gwamantin Nijeriyar ta yi da ta ƙasar, an sami cim ma matsaya da yarjejeniyar barin ‘yan Nijeriya su ci gaba da shiga kasar ta UAE.
Kazalika, sanarwar ta ce daga yarjejeniyar har da ɗage haramcin bayar da izinin shiga UAE ga dukkan ’yan Nijieriyar dake son shiga kasa
Sanarwar ta ce za a iya fara neman bizar daga 15 ga watan na Yuli, ta kuma bukaci ‘yan kasar su yi nazari kan bizar ta hanyar ziyartar shafinta na intanet domin karin bayani.
PRNigeria Hausa