Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar babbar jam’iyyar hamayya ta PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa halin yunwa da ake ciki a Nijeriya manufofin gwamnatin APC karkashin jagorancin Tinubu ne su ka haifar da shi babu gaira babu dalili.
Wannan na cikin wata sanarwa da Alhaji Atiku Abubakar ya fitar kuma aka raba ga manema labarai a Nijeriya, wadda ta dora alhakin yanayin komajin rayuwa da Al’ummar kasar ke ciki na tsadar kayan masarufi kan kudirin shugaba Tinubu.
Atiku ya ce rashin samar da matsaya kan mafi karancin albashi da zai yi dai-dai da yanayin rayuwar da ake ciki, zai zama mummunar barazana ga rayuwar ma’aikata da iyalen su a matakan gwamnatocin tarayya, jiha da kananan hukumomin kasar.
A yanzu shugaba Tinubu na shirin ciwo bashin dala biliyan 2 kari akan dala kusan biliyan 3 da rabi, wanda ba a san manufar cin bashin ba, inda zargi yai kwari cewar bashin na tabbatar da walwalar fadar gwamnatin tarayya ne da manyan jami’an gwamnatin.
Jagoran yan hamayyar ya ce Wannan mummunan bashin zai kara yawan bashin da ake bin kasar zuwa kusan kimanin dalar amurka billiyan 100 wannan zai kara ma gembo gishiri wajen ta’azzara mummunan halin da jama’a ke ciki. Wannan ba karamin bakin labari ba ne.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 9 hours 41 minutes 43 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 11 hours 23 minutes 8 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com