Home General Kudurin kirkirar sarakuna 3 masu daraja ta 2 ya tsallake karatu a...

Kudurin kirkirar sarakuna 3 masu daraja ta 2 ya tsallake karatu a Majalisar Dokokin Kano

Majalisar jihar Kano
Majalisar jihar Kano

Kudurin kirkirar sarakuna masu daraja ta biyu ya tsallake karatun farko a majalisar dokokin Kano

Sabon kudurin ƙirƙirar sakaruna masu daraja ta biyu ya tsallake karatu na farko a zauren Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Sabbin Sarakunan da aka ƙirƙira dai sune na Rano, Ƙaraye da kuma Gaya.

A cewar ƙudurin, dukkansu za su kasance ne ƙarƙashin Sarkin Kano, wanda shi kaɗai ne mai daraja ta ɗaya yanzu a jihar.

Kananan hukumomin da za su kasance ƙarƙashin Sarkin Rano sune Rano Kibiya da Bunkure, shi kuma na Karaye yana da kananan hukumomin Karaye da Rogo.

Matakin na zuwa ne bayan Majalisar ta rushe dokar da ta kirkiri sabbin masarautu guda biyar a jihar ta shekara ta 2019, tare da rushe sarakunan da aka naɗa musu.

Daga bisani dai Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya dawo da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II kan kujerarsa, inda ya sauke Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan guda hudu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Kwamitin Bincike Kan Mutuwar Ma'aikatan Haƙar Ma'adinai 37 a Hukumar Kula da Haƙar Ma'adinai ta NSCDCMajalisar Dattawa ta 10 da Ma'anar Jagorancin Majalisa Daga Kabir AkintayoDarakta Janar na NITDA ya yi Kira da a Hada Hannu Kan Tsarin AI a Taron Manyan ShugabanniƳancin Sanin Gaskiya: Bayani Game da Tsarin Gudanar da Harkokin Sadarwa na Najeriya Daga Franklyn Ginger-EkeHOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna Yusuf
X whatsapp