Home General Gwamnan Kano ya mayar da tsohon Sarkin Gaya kan kujerarsa

Gwamnan Kano ya mayar da tsohon Sarkin Gaya kan kujerarsa

Biyo bayan sanya hannu da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi na dokar Samar da masarautu masu daraja ta biyu a jihar Kano. Gwamnan ya amince da nadin Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, a matsayin Sarkin Karaye, wanda kafin wannan nadin ya kasance Hakimin karamar hukumar Rogo.

ta cikin wata takardar sanarwa da daraktan yada labaran Gwamnan jihar Sunusi bature Dawakin tofa ya fita, tace nadin ya fara aiki nan take.

Har ila yau, Gwamnan ya amince da nadin Alhaji Muhammad Isa Umar a matsayin Sarkin Rano Mai daraja ta biyu wanda shima kafin nadin ya kasance Hakimi a karamar hukumar Bunkure.

Sai Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin Sarkin Gaya Mai daraja ta biyu wanda dama shine tsohon sarkin Gaya da aka rushe.

A lokacin da yake taya sabbin Sarakunan murna, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarce su da su kasance masu kula da al’adu da zaman lafiya da kokari wajen kawo hadin kan al’ummar Masarautun nasu.

PRNigeria Hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp