Home General Masu garkuwa sun saki mahaifiyar mawaƙi Rarara

Masu garkuwa sun saki mahaifiyar mawaƙi Rarara

Mahaifiyar fitaccen mawaƙin nan na siyasa, Dauda Kahutu Rarara, wato Hajiya Halima Adamu, ta shaƙi iskar ’yanci bayan ’yan bindigar da suka yi garkuwa da ita sun sako ta.

Mawaƙi Rararan ne ya tabbatar da sakin nata a shafinsa na Instagram, inda ya ce an sako ta ne da sanyin safiyar Laraba.

Ya bayyana godiyarsa ga Allah sannan ya gode wa sauran jama’a kan gudunmawar addu’o’in da suka yi mata bayan faruwar lamarin.

Sai dai bai yi bayani kan ko an biya kudin fansa ba kafin sakin nata ko kuma a’a.

A baya dai, rahotanni sun bayyana cewar masu garkuwar sun buƙaci a ba su Naira miliyan 900 kafin su sake ta.

Tun kusan mako uku da suka gabata ne dai wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka sace Hajiya Halima mai kimanin shekaru 75 a gidanta da ke ƙauyen Kahutu a ƙaramar hukumar Ɗanja ta jihar Katsina.

Rarara dai ya yi suna wajen waƙe ’yan siyasa, musamman na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.

A lokuta da dama, ya sha nuna cewa gwamnatin APCn tana iya kokarinta wajen magance matsalar tsaron da ta addabi ƙasar, ciki har da ta ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp