Home DUNIYA Sojojin Nijeirya sun hallaka ‘yan Ta’adda 125 a cikin mako daya -DHQ

Sojojin Nijeirya sun hallaka ‘yan Ta’adda 125 a cikin mako daya -DHQ

Shalkwatar rundunar sojin Nijeriya tace dakarunta sun sami nasarar hallaka ‘yan ta’adda 125, tare da kama 200, inda suka sami nasarar kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su a wasu mabambanta hare hare da suka gudanar a kasar cikin mako daya.

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da daraktan yada Labaran shalkwatar Manjo Janar Edward Buba ya fitar a ranar juma’a yayin da yake bayar da bayani kan ayyukan rundunar a birnin Abuja.

jaridar Emergency Digest ta ruwaito Buba na cewa dakarun sun kwato makamai 120, gami da alburusai 1,793, sai kuma bindiga kirar AK47 guda 56, da kuma bindiga kirar gida guda 26, da kuma bindiga kirar Dane guda 22 da wasu muggan makamai.

Ya kara da cewa Alburushin bindiga kirar AK47 guda 21, sai kuma radio baofeng guda 1, motoci 6 babura 11, kekuna5, wayoyin hannun guda 38 da kuma kudi da sukai miliyan 2.7 da wasu abubuwa na daga cikin wadanda dakarun sojojin suka sami nasarar kwatowa a hannun ‘yan ta’addan.

Ya yankin area maso gabas kuwa dakarun operation Hadin Kai sun sami nasarar hallaka ‘yan ta’addan 52 tare da kama 40 inda suka sami nasarar kubutar da 14 cikin wadanda suka yi garkuwa da su.

PRNigeria Hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp