Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, DSS ta yi gargaɗi dangane da shirin zanga-zangar matsin rayuwa a kasar.
Hukumar ta DSS ta ce tuni ta riga ta gano waɗanda suka kitsa ta da masu goyon bayan zanga-zangar, inda suka gargaɗe su da su sanya kishin ƙasa su dakatar da shirin zanga-zangar.
Gargaɗin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Dakta Peter Afunanya ya aike wa manema labarai. wadda ta ce hukumar ta DSS ta gano cewa wasu batagari na shirin karkatar da akalar zanga-zangar da manufar tayar da zaune tsaye a Najeriya.
Read Also:
Dakta Afunanya ya kuma yi zargin cewa burin masu kitsa zanga-zangar shi ne sauya gwamnati musamman ta tarayya.
“Masu kitsa zanga-zangar na son yin amfani da haddasa hatsaniya domin shafa wa gwamnatin tarayya da na jihohi kashin kaji da ɓata musu suna domin haɗa su da talakawa. Burinsu shi ne sauya gwamnati musamman ta tarayya.” In ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa ta duk da cewa ta gano masu kitsa zanga-zangar da masu ba su kuɗaɗe amma hukumar tana bin hanyoyin da doka ta tanada waɗanda ba na amfani da ƙarfi ba domin daƙile zanga-zangar.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 6 hours 43 minutes 15 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 8 hours 24 minutes 40 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com