Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas ta tabbatar da mutuwar mutum uku a lokacin da wani gini ya rufta a rukunin gidajen Arowojobe da ke yankin Maryland a jihar.
Babban sakataren hukumar, Dakta Olufemi Oke-Osanyintolu ne ya bayyana hakan ga Kamfanin dillanci labarai na kasa NAN, inda ya ce lamarin ya faru ne da tsakar daren ranar Alhamis.
Ya ce mutane ukun da suka mutu a lokacin faruwar lamarin duka ma’aikatan gini ne.
“Bayan samun labarin faruwar lamarin, jami’an hukumarmu sun gazaya wurin tare da gaggauta fara aikin ceto, inda suka zaƙulo gawarwakin mutum uku duka maza, da wasu mazan biyu da aka zaƙulo da ransu sai kuma wani mutum guda da ya maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan ginin da shi ma aka ceto shi”, in ji shi.
Ya kuma ƙara da cewa tuni aka garzaya da mutanen da aka ceto zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci. Tuni aka kai manyan motocin tono domin faɗaɗa aikin ceton.
Rushewar gini wata matsala ce da ake yawan samu Najeriya. Ko a farkon wannan wata ma, an samu ruftawar ginin wata makaranta a jihar Filato da ke tsakiyar ƙasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar yara fiye da 20, tare da raunata mutane da dama.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 15 hours 22 minutes 24 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 17 hours 3 minutes 49 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com