Home General Sojoji Nijeriya sun mamaye manyan titunan Abuja gabanin zanga-zanga a kasar

Sojoji Nijeriya sun mamaye manyan titunan Abuja gabanin zanga-zanga a kasar

Direbobi a kan babbar hanyar Keffi zuwa Abuja a ranar Litinin sun shiga tsaka mai wuya bayan da sojoji suka tare babbar hanyar domin gudanar da bincike kan motocin da suka nufi Abuja, babban birnin Najeriya.

Sojojin sun dasa shingen bincike a barikin sojoji na Sani Abacha kafin shataletalen AYA.

Jami’an tsaro dai ba su bayar da wata sanarwa ba kafin toshe titin lamarin da ya janyo cunkoson ababen hawa har zuwa gadar Nyanya, sama da kilomita 12 daga wurin binciken motocin.

Jaridar Emergency Digest ta ruwaito cewa ma’aikata da masu tireda da ke aiki a Abuja, suna zaune a wajen tsakiyar birnin a wurare kamar Nyanya da Karu da Maraba da Masaka.

Bayan shafe tsawon sa’oi a wuri ɗaya – babu gaba, babu baya, akasarinsu daga bisani sun yanke shawarar komawa gida.

Wasu matasa a Najeriya na shirya zanga-zangar gama-gari daga 1 ga watan Agusta saboda tsadar rayuwa da taɓarɓarewar tattalin arziki a ƙasar.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp