Home General Gwamnan Osun ya gargadi masu Zanga – Zanga a jihar

Gwamnan Osun ya gargadi masu Zanga – Zanga a jihar

Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya gargaɗi ƴan ƙungiyoyin fararen hula da al’ummar jihar su kauce wa hargitsi a lokacin zanga-zanga da ake shirin gudanarwa daga ɗaya zuwa 10 ga watan Agusta a jihar.

Gwamna Adeleke, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Prince Kola Adewusi tare da wasu ‘yan majalisar zartarwa na jihar Osun ya bayar da shawarar ne a wata tattaunawa da mambobin ƙungiyoyin farar hula na jihar a yau Talata.

Gwamnan ya ce duk da cewa ya san ƴan kasa na da ƴancin yin zanga-zanga, su tabbatar da cewa ba su saka rayuwar ƴan jihar cikin haɗari ba.

Gwamnan ya ce “kwanciyar hankali da lafiyar ƴan jihar Osun shi ne babban damuwarmu da abin da muka fi mayar da hankali a kai a zanga-zangar da ake shirin gudanarwa.”

“Babban burina a matsayin gwamnan wannan jihar shi ne mayar da jihar a matsayin babban misali mai kyau ga sauran jihohi,” in ji gwamnan.

“Saboda haka ne na shawarce ku ƴan jihar Osun da ku kasance masu biyaya ga doka da oda a lokacin zanga-zanga da kuma bayan zanga-zanagar, ba za mu amince da duk wani hargitsi ba da tashin hankali yayin da kuke gudanar da zanga-zanga.” in ji gwamnan.

Ƙungiyoyin fararen hula da sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu na jihar sun yaba wa gwamnan da gudanar da irin wannan tattaunawar inda suka ce sun amince za su yi biyayya ga doka da kuma tabbatar da an yi zanga-zangar cikin lumana.

PRNIgeria

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp