Gwamnatin jihar Kano ta musanta cewa ta kashe naira biliyan 10 wajen siyan kayayyakin Ofis cikin watanni uku na farkon shekara ta 2024.
wannan dai na kunshe ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar kano Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya sanyawa hannu kuma ya aikowa PRNigeria.
sanarwar ta ce ”Magana ta gaskiya labarin ba gaskiya ba ne, gaskiyar abun da muka kashe shi ne naira miliyan 596, don haka muna kira ga al’ummar jihar Kano da su yi watsi da labarin bashi da tushe ballantana makama”.
Read Also:
Idan za a iya tunawa a ranar laraba, jaridar “Sahara Reporters”, ta rawaito cewa gwamnatin jihar Kano ta kashe kimanin naira biliyan 10 wajen siyan kayan ofis.
”Ma’aikatar kasafi da tsare-tsare ta jihar kano ta fitar da rahoton yadda aka aiwatar da zangon farko na kasafin kudin jihar na bana a ranar 28 ga watan Yuli, 2024, babu shakka a adadin kudin da suka fitar akwai kuskure, amma ya kamata ayi musu uzuri saboda suma yan adam ne”. Inji Sanusi Bature
Ya ce matakin da gwamnatin Kano ta dauka na fitar da rahoton akan lokaci ya nuna yadda gwamnatin ta ke kokarin yin komai a bayyane ba tare da yin kunbiya-kunbiya ba.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 8 minutes 51 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 50 minutes 16 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com