Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar kano ta bayyana cewa za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi 44 a ranar 30 ga watan Nuwambar 2024.
Shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya bayyana hakan ga Manema labarai a kano, ranar laraba.
Read Also:
Idan za a iya tunawa tun bayan da kotun kolin kasar ta yanke wani hukunci dake tabbatar da bawa kananan hukumomin kasar ‘yancin cin gashin kai Kuma ta ce duk karamar hukumar da bata da zababben shugaba ba zata sami kuɗin ta ba. aka jiyo gwamnoni na yunkurin yin zaben inda wasu tuni shiri yayi nisa.
haka shima Gwamnan kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a kwamakin bayan ya bayyana cewa sun shirya domin gudanar da zaben kananan hukumomin a jihar.
PRNigeria Hausa