Ƴan majalisar wakilai 15 a ƙarkashin ƙungiyar The Economy Rescue Group”, sun nemi da a dakatar da shugaban rukunin kamfanin mai na Nijeriya Mele Kyari.
Ƙungiyar ta yi ikirarin cewa rashin tafiyar da tsare tsare karkashin jagorancin Kyari a NNPC ne ke jawo ƙalubalen da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke fuskanta.
Wannan na cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a Abuja kuma shugabanta ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Oredo, Esosa Iyawe, shi ne ya sanya mata hannu kuma aka saki a ranar Talata, inda ƙungiyar ta dage cewa a dakatar da Kyari har sai an samu sakamakon kwamitin hadin gwiwa na majalisar wakilai game da binciken kwakwaf da ake yi na kan harkokin man fetur game da halin da kamfanin mai na kasa ke ciki.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Mu ‘yan majalisa mai ɗauke da mutane 15 mun lura cewa ko shakka babu matsalolin da ake fuskanta a bangaren man fetur da iskar gas a gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya samo asali ne sakamakon gazawa da rashin gudanar da ayyukan hukumar ta NNPC a karkashin jagorancin Kyari. Don haka, don warware waɗannan matsaloli dole ne su yi murabus.
Haka kuma ƴan majalisar na zargin shugaban kamfanin na NNPC da sauran ma’aikatan gudanarwar da yi wa tsarin shugaban kasa na daidaita tattalin arziki mai lakabin “Renewed Hope Agenda” zagon kasa.
“Tunda sun kasa sauka da kansu, to bai kamata shugaban kasa ya yi kasa a gwiwa ba wajen dakatar da su har sai an gama gudanar da binciken da majalisar wakilai ke gudanarwa kan harkokin man fetur.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 13 hours 47 minutes 40 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 15 hours 29 minutes 5 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com