Rahotanni daga unguwar Gandun albasa da ke karamar hukumar birni a jihar kano, na tabbatar da cewa wasu matasa sun farwa wata makaranta mai suna Wada Sagagi, inda suka kwashi shinkafa mai rubutun gwamnatin tarayya a jikin buhunta.
Wasu mazauna unguwar sun ce, matasan sun shiga gidan ne da talatainin daddare, domin kwasar shinkafar da ake zargin wadda gwamnatin tarayya ta aiko ne domin rabawa mabukata a jihar.
Read Also:
Makarantar dai, na zaune ne a tsohon gidan shugaban ma’aikata na fadar gwamnatin Kano, Alh Shehu Wada Sagagi.
sai dai kawo yanzu shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano Shehu Wada Sagagi da ake zargin na da alaka da kayan, bai ce komai ba.
Amma shugaban makarantar Islamiyyar ta Wada Sagagi ya tabbatar da faruwar shigar matasan cikin makarantar tare da kwasar buhunhunan shinkafar.
Idan za a iya tunawa makwani biyu da suka gabata, gwamnatin tarayya ta ce ta turawa gwamnonin jihohin Kasar tirela 20 ta Shinkafa zuwa kowacce jiha domin rabawa talakawa don magance matsalolin matsin rayuwa da ake ciki a.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1240 days 4 hours 17 minutes 55 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1222 days 5 hours 59 minutes 20 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com