Tinubu- Bukatar mu Nijar, Mali da Burkina Faso su koma cikin ƙungiyar ECOWAS.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sake kira ga ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso da su koma cikin ƙungiyar ECOWAS.

Shugaban, wanda kuma shine shugaban ƙungiyar ta ECOWAS a lokaci guda na jadadda wannan roƙo ne lokacin da yake ganawa da manyan hafsohin tsaron ƙasashe mambobin ECOWAS a Abuja.

Ya ce babbar buƙatar ƙungiyar a yanzu shine dawo da ƙasashen cikin ECOWAS, la’akari da muhimmanci da suke da shi, musamman ta fannin tsaro.

A cewar sa, shugabancin Najeriya da kuma na ECOWAS a lokaci guda ya sanya jagorancin ƙungiyar ya kasance mai matuƙar tsauri a gareshi, don haka zai yi duk mai yiwuwa don ganin sun dawo cikin ƙungiyar ba tare da wani tashin hankali ba.

Shugaban na Najeriya ya gargadi ƙasashen kan cewa dagewar da suka yi na ƙin komawa ECOWAS ba zai haifar musu da komai ba illa koma baya, la’akari da cewa duk abinda za’a yi shi a ƙungiyance yafi armashi da kuma tasiri.

Daga nan kuma sai Tinubu ya yabawa shugabannin tsaron ƙasashe mambobin ECOWAS kan irin kwarewar aiki da suka nuna ta yadda har yanzu yaƙi bai barke tsakanin su da ƙasashen da suka yi iƙirarin ficewa daga ƙungiyar ba.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 14 hours 42 minutes 10 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 23 minutes 35 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com