Kungiyar dilalan man fetur ta kasar nan tace nan da makwanni uku masu zuwa matatar mai ta fatakwal zata fara aiki yadda ya kamata, domin cimma umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar na watan Agusta.
Haka kuma kungiyar tace matatar zata ke fitar da mai lita miliyan 10 zuwa miliyan 12 ga ‘yan kasuwa.
Contirolan ayyukan na kungiyar Zarma Mustapha ne ya bayyana hakan yayyin da yake ganawa da kafar yada labarai ta NTA, inda yace matatar man zata habaka samar da man a kasar nana daga lita miliyan 11 zuwa 15 a ko wacce, gami da samar da wadataccen makamashi.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Haka kuma matatar zata yi aiki ne bisa zaman kanta, kuma zata sayar da man ne bisa farashin kasuwa ba tare da gwamnatin tarayya tayi mata katsandan ba.
Ko da yace bayan bayyana wannan kudiri Al’ummar kasar nan sun bayyana cewa sun gaji da gafara sa basu ga kaho ba, duba da yadda aka yi ta yi musu alkawurra amma babu guda daya da aka cika akan matatun na kasar nan.
Idan dai za’a iya tunawa mahukunta a kasar nan sun bayyanawa al’umma cewa matata zata fara aiki watan disambar 2023, idan aka hada da wannan alkawari gwamantin tarayyar kasar nan tayi alkawarin sau hudu kenan tun bayan darewarta kan karagar mulki.
PRNigeria hausa












