SERAP ta bukaci Tinubu ya binciki bashin dala biliyan 1.5 da jihohi 36 suka karbo

Kungiyar  dake yaki da cin hanci da daidaito na harkokin gwamnati SERAP ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya binciki bashin dala biliyan 1.5 na bankin duniya da jihohi 36 suka karbo tare da babban birnin tarayya.

Kungiyar ta kuma bukaci Tinubu da ya binciki zargin karkatar da lamunin China na $3.121bn da gwamnatin tarayya ta tarba.

SERAP ta roki Shugaban kasa da ya umarci Babban antoni janar na kasa kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, da hukumomin da suka dace da yaki da cin hanci da rashawa da su gaggauta yin bincike sosai kan yadda aka kashe rancen, ta yadda za a rage “talauci da inganta rayuwar al’umma a fadin jihohin kasarnan.”

Hakan na kunshe ne a wata budaddiyar wasika mai kwanan watan Agusta 10, 2024, mai dauke da sa hannun Mataimakin Daraktan kungiyar, Kolawole Oluwadare.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1189 days 15 hours 27 minutes 11 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1171 days 17 hours 8 minutes 36 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com