Home Labarai Ana fargabar mutuwar Mutane 16 sakamakon kifewar kwale-kwale a jihar Sokoto

Ana fargabar mutuwar Mutane 16 sakamakon kifewar kwale-kwale a jihar Sokoto

Akalla mutane  16 ne suka ake zargin sun mutu bayan wani kwale-kwale makre da mutane ya kife a jihar sokoto dake arewa maso yammacin Nijeriya.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Dundaye inda hukumar agajin gaggauwa ta NEMA ta bayyana cewa akwai mutane 19 da suka tsira da rayukansu.

Kwale-kwalen na ɗauke da manoma ne inda zai kai su gonakinsu na shinkafa a ranar Lahadi.

An gano gawa guda, sannan kuma akwai mata da yara daga cikin waɗanda suka ɓace.

Masu ninƙaya da kuma masu kamun kifi na cikin waɗanda suka shiga aikin ceton.

Jami’ai sun ce jirgin ya ɗauko ninkin mutanen da ya kamata ya ɗauka ne.

A makon daya wuce ma wasu manoma 15 sun nitse bayan jirgin ruwan da ya ɗauko su ya kife a jihar Jigawa da ke arewacin Nijeriya.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp