Babban kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL, ya ce ya bankaɗo wuraren 63 da ake tace mai fetur ba bisa ƙa’ida ba a cikin makon da ya gabata.
Cikin wani rahoton kamfanin da aka yaɗa a gidan Talbijin na ƙasar NTA, ya nuna cewa an gano haramtattun bututan mai 19 da kuma wurare 63 da ake tace mai ba bisa ƙa’ida ba.
Rahoton kamfanin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan jinkirin fara aikin matatar mai ta birnin Fatakwal, ba kamar yadda aka tsara tun farko ba.
Matatar ta Fatakwal – da ke ƙarƙashin kamfanin NNPCL – ta kasa fara aiki bayan an ɗage lokacin fara aikin nasa har sau shida.
Ma’aikatar albarkatun man fetur ta Najeriya da kamfanin mai na NNPCL sun alƙawarta fara aikin matatar cikin wannan wata, to sai dai alamu na nuna cewa ba lallai ne matatar ta fara tace man cikin wannan wata ba.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 57 minutes 51 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 39 minutes 16 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com